Wani matashi dan shekara 21 mai suna Temple Samuel da ‘yan sanda suka kama shi a jihar Legas, ya bayyana cewa ya siyar da Motar ubangidansa mai suna Lexus 330 ne don biyan kudin tafiyarsa zuwa kasar waje.
Wanda ake zargin tare da wasu mutane uku da aka kama a unguwar Ogba da ke jihar, ya ce, “ Na yi Niyyar guduwa da motar oga na be, domin in sayar, kuma inyi amfani da abin da aka samu wajen tafiyata zuwa kasashen waje. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
“Na dade ina son fita daga kasar nan don in je neman kudi. Rayuwa ba ta da sauƙi a Najeriya shi ya sa na so in sayar da motar.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Tsare Wani Mutum Da Ya Kashe Kaninsa Da Duka
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya bayyana sauran wadanda aka kama tare da Samuel, Benjamin Bassey mai shekara (32), Chukwuemeka Okorie (29) da Joshua Agboche (37).
Hundeyin ya ce Samuel da mutanen uku sun hada baki ne wajen sayar da motar.
Ya ci gaba da cewa bincike ya nuna cewa Samuel wanda ke aikin wankin motar maigidan nasa a unguwar Egbeda, ya tuka motar ne da tsakar dare, tare da sace wayoyin Mai gidan kirar iPhone X da iPhone 13, kuma daga bisani ya kwashe Naira 75,000 daga asusun bankin Maigidan nasa.
Hundeyin ya kara da cewa, “Wanda ake zargin ya kammala shirye-shiryen yin amfani da kudaden da ya samu na siyar da motar da sauran kayan da ya sata wajen tafiyarsa zuwa kasar waje.”
A WANI LABARIN KUMA: Yan Sanda Sun Kama ‘Yan Fashi 3 A Jihar Benue
Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami da miyagun kwayoyi da kuma kasancewa mambobin kungiyoyin asiri.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.