Matashiyar nan da ta yi shura a shafin Tuwita Mai duna Khadija wacce ta fito ta bayyana irin ka’ida da za ta baiwa mijinta ta ce ta yi nadama.
Cikin wani sako da ta wallafa a shafin nata na Tuwita a kwanakin baya, ta bayyana cewa matukar za ta yi aure, to dole mijinta ya tabbatar da cewa mamanshi ba za ta zauna a gidansu ba har na kwanaki uku.
“Duk wanda zai aure ni, to dole ya amince da ka’idata cewa mamansa ba za ta zauna a gidan da za mu zauna ba har na fiye da tsawon kwana uku, Maganar Gaskiya kenan”
Ko da yake ba ta bayyana irin dalilinta na yin haka ba, to amma jama’a da dama sun yi sharhi kan wannan batu nata inda wani bangare mai girman gaske na ganin abin nata azimun ne.
Ita dai Khadijah matashiya ce wacce da ganinta ka san son kowa ce ƙin wanda ya rasa, wata kila hakan ne wasu ke ganin ya sanya ta wannan aika-aika.
Ko da yake daga bisani kamar matashiyar ta goge rubutun nata bayan ganin ruwan maganganu masu dadi da akasin haka, amma rubutun ya janyo cece-cece cuki da wajen tuwita.
Cikin wani sakon tuwita da ta sake wallafawa, Khadija ta nemi afuwar mabiyanta tare da bayyana cewa ba ta yi hakan da wata manufa ba face don raha, amma ta gane kuskuren ta.
To ko ma dai da wasa take yi, lamarin zaman uwar miji a gidan danta na zama wa matan wannan zamani tamkar karfen kafa ne, inda har tuni da ma suka sa mata suna da Olsa (Ulcer).