Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya bayyana nadamarsa game da yin yafiya ga masu aikata laifukan fyaɗe a jihar a lokucin dokar kullen Korona.
Idan ba a manta ba hukumar ‘yan sanda a jihar Bauchi sun kama wani mutum mai suna Yusuf Bako da laifin yiwa yarinya ‘yar shekaru huɗu a duniya fyaɗe a masallaci.
Bako yana ɗaya daga cikin wanda gwamnatin jihar Bauchi ta yafewa laifukan da suka aikata.
https://dimokuradiyya.com.ng/fyaɗe-wani-mutum-mai-shekaru-61-a-duniya-ya-yiwa-yarsa-cikin-shege/
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da kwamitin yaƙi da laifukan fyaɗe ƙarƙashin jagorancin Hajiya Aisha Mohammed suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin jihar.
“Dole ne mu nemi afuwar mata bisa faruwar wannan kuskuren, dana dan cewar har da shi a cikin wanda zan yafewa to, tabbas da ba zai fita ba har sai wa’adinsa ya ƙare” cewar gwamna Bala.
Sannan gwamnan ya ƙara jan kunne masu aikata laifin Fyaɗe cewa gwamnatinsa ba zata ɗaga musu ƙafa ba.