Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya bayyana jin dadinsa da irin matsalolin rikici da jam’iyyar APC take, saboda a cewarsa wannan ita ce hanya ɗaya da jam’iyyarsa ta PDP zata iya dawowa kan karagar mulki a kasar nan.
Wike ya bayyana haka ne a wata tattaunawarsa a shirin siyasa na gidan talabijin din Arise. Da aka yi masa tambaya game da ra’ayinsa dangane da dawowars Obaseki Jam’iyyar PDP, gwamnan ya bayyana cewa yaji dadi matukar saboda duk abinda ya shafi kudu masu kudu a kasar nan ya kamata su kasance a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.
“Idan ka tambayeni ko ina murna, tabbas zan ce maka ina farin ciki domin da halin da APC take, kuma bana fatan ace komai ya daidata, saboda mu ma a lokacin Ali Modu Sheriff mun samu matsaloli marasa adadi kuma su ma dadi suka ji”.
“A matsayina na dan siyasa burina su ci gaba da samun matsala, domin wannan ita ce hanya guda daya da jam’iyya ta zata iya dawowa kan mulki”.