Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da shugabannin kwamitin ayyuka don gudanar da yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa nan jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa kwamitocin da aka nada shugabanninsu sun hada da Sokoto, Zamfara, Kebbi, wadanda suka kunshi manyan mutane yan kasuwa, don ganin sun bayar da duk gudunmawar data kamata, wajen nasarar dan takarar su.
Shugabannin yankunan an kuma shawarci su, kan suyi duk mai yiwuwa wajen sake nemo magoya baya ga yan takarar jam’iyyar PDP.
A yayin taron kaddamar da shugabannin wanda ya gudana a cibiyar taruka ta kasa da kasa dake Ƙasarawa, Tambuwal ya godewa duk wanda ya bayar da gudunmawa wajen hada yan kasuwar don aiki tare da nufin samun nasarar PDP a zaben baɗi.
KARANTA ANAN: Ku Sanya Bukatun Al’ummar Kano A Gaba Sama Da Bukatar Kai – Farfesa Munzali
Ya kara da cewa matukar Atiku yayi nasara a zaben, yana da tabbacin bangaren tattalin arzikin Najeriya zai koma hayyacinsa.
A nasa jawabin guda cikin iyayen kwamitocin Sanata Abdul Ahmad Ningi, ya yaba da samar da tsarin, tare da cewa wannan yunkuri zai taimaka wajen nasarar jamiyyar a zaben 2023.
A wani labarin kuma: Ɗan Shekara 18 ya mutu a Ruwa, a lokacin da yake Ƙoƙarin ceto Saniya a Jigawa
Wani yaro Ɗan Shekara 18 mai suna Adamu Musa ya mutu a kokarin ceto saniyar sa a karamar hukumar Buji ta jihar Jigawa.
Wani mazaunin garin ya shaidawa DAILY POST cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a Unguwar Magina da ke cikin garin Buji.