Fitaccen masani kuma malamin turancin nan farfesa Munzali Jibril ya ce koyar da dalibai cikin harshen Hausa shi ne kadai mafita ga matsalar ilimi a Arewacin kasar nan.
Munzali Jibril ya bayyana hakan ne yayin taron wuni daya da dukkanin yan takarar gwamman a dukkanin jam’iyyu domin gabatar musu da manufofin da za su ciyar da Kano da Jigawa gaba.
Taron wanda Zauren kwarraru na Kano da Jigawa wato (Kano Jigawa Professional Forum) ya shirya na da manufar kawo gyara kan yadda ake tafiyar da al’amura a jihohin biyu.
Farfesa Munzali ya ce dalibai da dama na da hazaka da za su iya karatu mai zurfi Amma turanci na dakilesu.
Ya ce tunda dai karatun Firamare da na karamar sakandire na hannun gwamnatocin jihohi to ya kamata su sauya tsarin.
KARANTA ANAN: Tinubu Yana Mamakin Dalilin Da Yasa Har Yanzu PDP Take Wanzuwa
A cewarsa a yanzu dalibi zai gama makaranta ya kuma samu sakamako amma da za a sanyashi ya rubuta layi daya na turanci ba zai iyaba.
Adon haka ya ce zauren yana bada shawara ga masu ruwa da tsaki da su mayar da harshen uwa wanda za a dinga yin amfani dashi a makarantun firamare da na karamar sakandire.
Da yake nasa jawabin daya daga cikin ‘yan takarar gwamnan Kano kuma mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna ya ce matukar ya samu nasara to ba shakka zai yi amfani da shawarwarin da zauren ya bayar.
A cewarsa bakaramin tunani aka yi ba wajen fitar da tsare-tsaren da ake ganin za su ciyar da Kano gaba.
A wani labarin kuma: Gobarar Tankar Mai Ta Kone Gine-gine 10 A Ogun
Gobara ta kone gidaje 10 a lokacin da wata tankar mai dauke da lita 45,000 na fetur ta kama da wuta a Ifo da ke jihar Ogun.
Daiky Trust ta ruwaito cewa, Wata sanarwa da Mista Ibrahim Farinloye, ko’dinetan shiyyar Kudu maso Yamma, na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ya fitar a jiya, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na safe a kan titin Olambe Matogun, Ifo.