Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya ce ko tantama babu nasarar da Jam’iyyar su ta samu cikin kankanin lokaci ya dama wanda Jam’iyyar PDP ta yi cikin shekara 16 tana mulkar kasar nan.
Yahaya Bello wanda ke wannan bugun kirji a wani shiri na tashar talabijin na Channels mai suna Sunrise Daily, ya ce ko bai faɗa ba ma yan Najeriya shaidu ne sun san da haka.
Ya ce “Zan fada da kakkausar murya, abinda APC ta yi bahu hadi da shekara 16 na PDP, in Ji Yahaya Bello wanda yale wannan hira daga gidan Gwamnatin Jihar Kogi.
“Nasarorin APC cikin shekara shida ya dama na PDP na shekara 16. Akwai kididdiga kowa ya sani, za mu iya tunawa yan Najeriya yadda muka saku kasar nan, da kuma yadda take a halin yanzu”.
Bugu da kari gwamnan ya ce tun bayan da PDP ta dare karagar mulki a farkon shigowar Dimokuradiyya a 1999, komai na kasar nan sai tavarbarewa yake ta yi, har sai bayan da APC ta fatatake ta a shekarar 2015.
Yahaya Bello ya kuma tabo batun matsalar tsaro da har yanzu ke ci gaba da daurin huhun goro wa kasar nan, inda ya bukaci yan Najeriya da su tashi tsaye su rungumi dabi’ar taimakawa wajen ganin an shawo kan lamarin.