Osun: Kotu ta Ɗaure Tsohon Kwamandan Matasa Masu yiwa Ƙasa Hidima Shekaru 2 kan satar 3.1m
Mai Shari’a Ojo na Babbar Kotun Jahar Osun ta 1 dake Osogbo ya ɗaure tsohon Kwamandan tsawatar da Matasa Masu Yiwa Ƙasa Hidima Mr Sola Oyedeji na tsawon shekaru biyu da aiki mai wahala kan Satar Naira miliyan 3.1 kuɗin da aka ware domin Albashin Matasa Masu yiwa Ƙasa Hidima.
Hukumar Hana Almundahana ta Kama Oyedeji a ƙarƙashin Sashe na 390 dana 467 da manyan laifuka tare da kaishi Kotu da tuhume-tuhume guda 10.
Ɗaurarren, wanda aka fara shari’ar sa a Shekarar 2011, an tuhume shi da kasa biyan Albashi na Mambobin masu Yiwa Ƙasa Hidima a Shekarar 2007, bayan Gwamnati ta sakar mashi su.
A cikin wata Sanarwa da Hukumar ICPC ta fitar a ranar Lahadi a tabakin mai Magana da Yawun ta Mrs Azuka Ogugua tace “An zargi Oyedeji da sace kuɗin sakamakon rashin biyan Albashin mambobin a watan Mayu na Shekarar 2007 bayan Gwamnatin Jaha ta turo mashi su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu Yanzu: Ƴan bindiga sun kai hari ga Jami’an Hukumar FRSC ta Anambra, sun Kashe Mutum 2
“Mai Shari’a Ojo ya yanke masa hukuncin Ɗaurin Shekaru biyu da aiki mai wahala, da kuma zaɓin biyan tara na Naira dubu 100,000 ga duk tuhuma ɗaya da ake yi mashi, tare da maido da kuɗin ga Asusun Hukumar na Jahar. Hukuncin ya fara aiki nan take.
Comments 1