Babban Jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele yayi murabus daga mukamin sa cikin gaggawa.
Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan ne yayi wannan kiran, lokacin da yake zantawa da manema labarai a yau Alhamis a Sakatariyar Jam’iyyar ta Kasa da ke Babban Birnin Tarayya Abuja inda ya ce, lokacin Emefiele a matsayin Gwamnan Babban Bankin CBN a karkashin gwamnatin jam’iyar APC ya sa Gwamnati na fuskantar matsalar tsare-tsare na kudade a kasar nan, inda ya bukaci ya sauka daga mukaminshi.
Ologbondiyan ya ce, abin koyi ne a lura cewa lokacin da Emefiele ya hau kujerar Gwamnan Babban Bankin Najeriya a shekarar 2014, an canza Dala zuwa Naira 164 a Nigeria.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ruftawar Gini ya yi sanadiyar mutuwar Mutum guda da jikkata wasu a Rivers
“A yau, a hannun Emefiele da kuma Jam’iyar APC, Naira ta durkushe zuwa kusan Naira 600 zuwa Dala, Wanda hakan ya nuna ta durkusar da tattalin arzikin kasar nan.” Inji shi.
Ya kara da cewa, “A karkashin jagorancin Emefiele, CBN ta gaza a aikinta na sarrafa tattalin arzikin kasar nan, tare da yin wasu ikirarin da basa nuna hakikanin gaskiyar da tattalin arzikin kasar nan ke ci,” a cewar shi.
Comments 1