Tsohon sanata kuma jigo a jam’iyyar PDP a jihar Yobe Alh. Adamu Garba Talba, ya sake ficewa daga jam’iyyar ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
Wannan dai na zuwa ne watanni biyu bayan da Sanata Talba ya koma PDP daga APC.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sojoji Sun Hallaka Wanda Ya Kitsa Harin NDA Ta Kaduna
A wata sanarwa a ranar Asabar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Gwamna Buni, Mamman Mohammed, ta nuna cewa Sanata Talba ya ce ya koma jam’iyyar APC ne domin ya gane irin gagarumin ci gaban da gwamnatin APC ta samu a jihar da kuma tabbatar da ci gaba.
Ya ce, “Babu wata fata ga jihar Yobe da Najeriya a wata jam’iyyar siyasa sai APC.”
“Ina nan a APC don alheri da ci gaban jihar Yobe da Najeriya”.
Gwamna Mai Mala Buni, wanda ya tarbi tsohon dan majalisar, ya bayyana sauya sheka Talba zuwa APC a matsayin zuwa gida.
“Maganar gaskiya, babu wani wuri mafi kyau gare ku da sauran ’yan Yobe kamar APC. Dukkanmu muna da rawar da za mu taka da kuma gudummawar da za mu bayar don samar da babbar jihar Yobe da Najeriya,” in ji Buni.
Gwamnan ya bayyana fatansa na cewa wanda ya sauya sheka zai bayar da gudumawa wajen wadata jam’iyyar, gina Yobe da kuma ci gaban Nijeriya.
Idan za a iya tunawa, Sanata Adamu Talba ya wakilci mazabar Yobe ta Kudu a majalisar dattawa ta 6 daga shekarar 2007 zuwa 2011 a karkashin jam’iyyar PDP.
A wani labarin kuma, Kama Mamu Ta’addanci Ne Gumi Ya Caccaki DSS
Malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kira ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta saki Tukur Mamu, ko kuma ta gurfanar da shi a gaban kotu.
Da yake bayar da misali da dokar, Gumi ya ce duk wanda aka kama bisa aikata laifin akwai bukatar a gurfanar da shi gaban kotu cikin sa’o’i 24.