Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa duk mai hannu cikin hatsarin jirgin da ya yi sanadiyar mutuwar Hafsan Sojin Najeriya Manjo Janar Ibrahim Attahiru lallai zai dandana kudarsa.
Yayin mika ta’aziyarsa ga iyalan mamacin Shugaba Buhari ya bayyana cewa lallai kasar nan ta yi babban rashi wanda maye gurbinsa ba abu ne mai sauki ba.
A Jiya Juma’a ne dai Attahiru ya gamu da Ajalinsa a yayin hatsarin jirgin sama a hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja tare sa wasu mutane goma da dukkannin su babu wanda ya yi rai.
Wata sanarwa da Kakakin Shugaba Buhari kan yada labarai Femi Adesina ya fitar, ta ce bincike ne zai tabbatar da Musababbin hadarin jirgin, kuma rayin su ba zai tafi a banza ba.
A watan Janairun Wannan shekara ne dai Shugaba Buhari ya nasa Attahiru wanda ya maye gurbin Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai wanda ya yi ritaya.