Dan wasan baya na Super Eagles Tyronne Ebuehi ba zai buga wasan da Venezia za ta yi da Bologna a gasar Seria A yau Lahadi ba.
Matashin mai shekaru 25 ya samu rauni ne a cinyarsa ta dama, wanda hakan ya sa ba zai buga wasan da kungiyar tasa zata yi a yau ba.
“Game da wasan da Bologna, ba za mu iya cewa akwai wani sabon labari mai dadi ba, labari mara kyau ya zo daga Tyronne Ebuehi. ”
“A gaskiya dan wasan baya na Najeriya ya tsaya kuma gwaje-gwajen kayan aiki sun nuna cewa, ya sami rauni a cinyarsa ta dama.
“Har yanzu ba a tantance lokutan murmurewarsa ba amma tabbas za a dauki ‘yan makonni kafin ya dawo fagen wasanni, a wasan zamu buga da tsohuwar kungiyarsa ta Benfica,” a cewar www.tuttoveneziasport.it.
Ebuehi ya koma Venezia ne a matsayin aro daga Benfica ta Portugal a bazara.
Ya buga wa kungiyar wasa sau takwas a gasar Seria A da daya a gasar cin kofin Italiya