Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya dage cewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorcha Ayu, ba zai iya jagorantar jihar wajen yakin neman zaben 2023 ba.
Wike ya yi wannan maganar ne a wajen kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar PDP na jihar Ribas na 2022 tare da kaddamar da dan takarar gwamna na jam’iyyar, Sim Fubara, a filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke Fatakwal, ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Mun Yi Shirin Ko Ta Kwana Don Zuwa Zagaye Na Biyu A Zaben — INEC
Gwamnan ya ce mutanen jihar Ribas sun ji rauni ne saboda rashin adalcin da ake yi wa jihar.
“Na sake maimaita cewa Ayu yana cin hanci da rashawa. Mutumin da ke cin hanci da rashawa ba zai iya shugabantata ba kuma ba zai iya jagorantar jiha ta zuwa yakin neman zaben shugaban kasa ba,” in ji Wike.
A WANI LABARIN KUMA: EFCC Za Ta Daukaka Kara Kan Korar Karar Zargin Almundahanar Da Ake Wa Babachir Lawal
Hukumar EFCC ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin da mai shari’a Charles Agbaza na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya yanke ranar Juma’a, wanda ya yi watsi da karar da ake yi wa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Mista Babachir Lawal.
Da yake yanke hukunci kan karar da aka shigar kan Babachr Lawal da sauran wadanda ake tuhumar, mai shari’a Agbaza, ya ce hukumar EFCC da ta gabatar da shaidu 11 a shari’ar ta kasa gabatar da hujjojin zargin aikata laifin.
Ya ci gaba da cewa, EFCC ba ta tabbatar da cewa Lawal mamba ne a kungiyar Presidential Initiative for North East da ta bayar da kwangilar ba.