Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta gabatar da Cek din kudi na kimanin naira miliyan 22 da dubu dari 7, ga iyalan jami’an 15, da suka mutu abakin aikinsu a jihar.
Da yake gabatar da makudan kudade ga makusantan jami’an da suka rasu a Shelkwatar rundunar yan sandan jihar dake garin Lafia, a jiya Alhamis, Kwamishinan yan sandan jihar Nasarawa Mista Adesina Soyemi, ya bayyana cewa, daukar matakin wani shiri ne na Sufeto-Janar na yan sanda na Kasa Usman Baba, wanda ake yiwa lakabi da “Tabbatar da Rayuwar Jami’ai “, da nufin tallafa wa iyalan jami’an da suka mutu a cikin hidimar aikin Dan sanda.
Ya Kara dacewa, “Anyi hakan ne don a kara wa sauran jami’an yan sandan kasar nan kwarin gwiwa, ta yadda za su yi iya kokarinsu wajen yaki da miyagun laifuka, don tabbatar da cewa, ankare kasar daga runkan barazanar tsaro .” Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Filato ta yi Allah Wadai da kisan Dalibin Kwalejin jihar
Da take zantawa da majiyar jaridar Dimokuradiyya, daya daga cikin wadanda suka amfana wannan Shirin, Misis Nformi Emerencia, ta yaba wa rundunar yan sanda, tare da yin alkawarin yin amfani da kudin kamar yadda ya dace.