A wani mataki na ci gaba da bada tsaro ga yankin da matsalar tsaro ta ɗaiɗaita shi, rundunar yan sandar jihar Kaduna ta tura daruruwan jami’anta a wadannan yankuna.
Kazalika matakin tura jami’an yan sandan shine don bada kariya ga manoma don samun zuwa gonakinsu yadda ya Kamata, la’akari da yadda ake fuskantar karancin abinci.
Ba nan kaɗai ba, har wa yau an umarci jami’an shiyoyi a jihar da su tura jami’an su zuwa makarantu dake fuskantar da matsalar tsaro a yankinsu.
Wannan umarni na zuwa ne daga bakin Kwamishinan yan sandar Jihar mai barin gado CP Umar Muri, yayin da yake gabatar da wasu da ake zargi da laifin aikata laifukan ta’addanci daban daban a jihar.
Umar Muri ya ce rundunar yan sandar jihar karkashin kulawarsa, ta cafke muggan mutane kimanin 500 kana ta ceto wasu shanu da adadin su ya kai kimanin 700.
Daga bisani ya ja hankalin sarakunan gargajiya da su tashi tsaye wajen hada karfi da karfe da jami’an yan sanda da ma sauran jami’an tsaro don gudu tare a tsira tare.