Rundunar yan sandan jihar Osun ta tabbatar da garkuwa da matafi a garin Ede kusa da Imesi-Ile na karamar hukumar Obokun dake jihar.
Jami’ar hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar SP Yemisi Opalola ne ta tabbatar da hakan a yau Talata a garin Osogbo, inda ta ce, yan bindigan sunyi garkuwa da matafiyan ne da yammacin jiya Litinin.
A cewar Opalola Babar Motar dake jigilar matafiya zuwa wasu jihohin, ta taso ne daga jihar Ekiti za ta zo Osun, inda yan bindigan suka tsayar da ita, da karfin tuwo, a iyakar jihohin biyu.
Jami’iar ta kuma ce, wasu daga cikin fasinjojin sun tsira daga lamarin, ya yin da yan bindigan suka yi garkuwa da wasu daga cikin su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kashe Mutum biyu a Katsina
Kazalika ta ce, haryanzu dai ba’ fayyace adadin mutanan da a kayi garkuwa da su ba.
Ta kuma ce, Tawagar jami’an yan sanda da na yan sankai, sun bi sahun masu Garkuwa da mutanan, domin ganin an ce to fasinjojin.
Opalola ta kuma ce, Kwamishinan yan sandan jihar Mr Olawale Olokode ya bai wa jami’an yan sandan umarnin cewa, su tabbatar sun kama masu Garkuwa da mutanan.
Comments 1