Rundunar Yan Sandar Jihar Ebonyi dake kudancin kasar ta dakile wani yunkurin kai hari wa ofishin ta inda ta yi nasarar hallaka daya daga maharan.
Kakakin Rundunar DSP Loveth Odah ita ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a birnin Abakalke a yau Lahadi.
Ta ce maharan sun zo ne a wata mota kirar Mitsubishi inda suka haura ta katangar Shelkwatar yan sandar ns Ugbuofo dake karamar hukumar Ebonyi.
Loveth ta jaddada cewa bayan shigar su ofishin ne fa suka fara luguden wuta a kan mai uwa da wabi, to amma jami’an yan sanda dake bakin aiki sun yi nasarar kakkabe su, inda har suka hallaka daya daga cikinsu.
Baya ga nan kuma ta ce an yi nasarar karbe bindiga kirar AK47 da da wayoyin salula gami da wukake banati yayin da wasun su kuma suka tsira da raunukan alburushi.
Kuma tuni Kwamishinan yan sandar Jihar Mista Aliyi Garba ya ziyarci inda al’amarin ya faru don ganin irin ta’adi da aka yi.
Da ma dai a yan baya-bayan nan yankin Kudancin kasar nan ya yi kaurin suna wurin hare-haren Ƙungiyar yan bindiga ta Inyamurai wato IPOB.