Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya soke tafiyarsa da ya shirya zuwa Landan don duba lafiya.
Da ma dai an tsara a ranar Juma’ar nan ne shugaba Buharin zai kai ziyarar duba lafiyar tasa.
Mai taimakawa Shugaban kasar kan yada labarai Femi Adesina wanda shine ya sanar da wannan mataki cikin wata sanarwa, ya ce nan gaba kaɗan za a sake sanar da ranar Buharin zai yi wannan tafiya.
A ranar Alhamis ne Adesina ya sanar da cewa shugaba Buhari zai tafi Landan kana zai dawo a mako na biyu cikin watan gobe.
Kimanin watanni uku kenan dai rabon shugaba Buhari da kasar ta Birtaniya inda can duba lafiyar tasa yaje.