A ranar Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dakta Duke Okoro a matsayin shugaban Kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya dake Orogun a karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege ne ya gabatar da kudurin nadin Shugaban Kwalejin na Orogun kuma majalisar ta amince da shi a matsayin doka.
KANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: An Jibge Tarin Jami’an Tsaro A CBN
Daga bisani shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da da nadin.
An yi la’akari da yadda shugaban kasa ya amince da nadin Okoro a matsayin shugaban Kwalejin.
Kafin nadin nasa , Okoro ne Daraktan ci gaban kasa da kasa a Jami’ar Tarayya ta Albarkatun Man Fetur da ke Effurun Jihar Delta.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: An Jibge Tarin Jami’an Tsaro A CBN
Akwai jami’an tsaro sosai a babban bankin Najeriya (CBN), reshen Abeokuta.
Yan sanda da sanyin safiyar ranar Litinin, sun tura jami’ansu zuwa reshen bankin Apex da ke Okelewo, Abeokuta domin dakile yiwuwar kai hare-hare daga masu aikata laifuka