Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na duba yiwuwar ƙara wa’adin amfani da tsofaffim kuɗi, har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun 2023.
Shugaba Buhari na tunanin ƙara wa’adin ne domin bin umurnin kotun ƙoli da kuma sauƙaƙewa ƴan Najeriya wahalhalun da suke sha a dalilin ƙarancin kuɗaɗen. Rahoton jaridar Legit.ng
KU KARANTA KUMA: Matashi ya samu sauyin rayuwa bayan ya taki sa’ar yin wuff da wata kyakkyawar baturiya
A cewar wata majiya mai tushe daga faɗar gwamnatin tarayya, shugaba Buhari ya damu kan matsalar da zata iya biyo baya ta fannin shari’a kan ƙin bin umurnin kotun ƙoli.
Wannan dai na daga cikin abubuwan da aka tattauna a wani zama da shugabannin ƙungiyar gwamnonin Najeriya da gwamnonin jam’iyyar APC, a ranar Laraba, 15 ga watan Fabrairu.
Majiayar ta bayyana cewa:
“Matsayar da aka cimma an same ta ne domin a ba shugaba Buhari damar yanke hukunci kan tsarin kuɗi sannan kuma ya bayar da waɗannan sanarwowin.” A cewar majiyar.
“Na ɗaya, cewa abar tsofaffin takardun kuɗi na ne, N1,000, N500 N200, su cigaba da shige da fice a cikin bankuna har zuwa nan da kwana 60.”
“Na biyu, cewa duka takardun kuɗin guda uku za a cigaba da amfani da su a matsayin halastattun kudi a cikin lokacin, amma duk tsohuwar N500 ko N1,000 da taa shiga banki to zata sake fitowa ba.”
Kin Amsar Tsofaffin Kudi: Zanga-Zanga Ta Barke A Ondo
A wani labarin na daban kuma, an samu barkewar zanga-zanga kan ƙin karɓar tsofaffin kuɗi a jihar Ondo.
Zanga-zangar ta barke a birnin Akure na jihar Ondo kan kin karbar tsoffin takardun kudi da bankunan kasuwanci suka yi. Kamar yadda The Nation ta ruwaito.
An fara zanga-zangar ne a bankin First Bank da ke Alagbaka, sakamakon fusatattun abokan huldan Banki da suka shafe sa’o’i da dama ba tare da zuwa wurin aikin ba.