Yayin da yan adawa ke ci gaba da sukar lamirin shugaban kasar Zambia Edgar Lungu, a Litinin din na ya bada umarnin jibge jami’an soji yayin da ake dab da gudanar da zaben gama gari a kasar.
Ya ce yanzu haka tuni an jibge jami’an sojin a Lusaa babban birnin kasar kuma za a tura karin wasu izuwa Sassan kasar daban-daban, don taimakawa jami’an yan sanda wajen dakile Matsalar tsaro da zaben zai haifar.
Sai dai Jam’iyyar adawa ta APC ta ce wannan mataki an dauke shi ne don sanya fargaba a zukatan al’umma musamman yan adawa.
Da ma dai an samu barkewar hatsaniya tsakanin jam’iyya mai mulki da kuma magoya bayan yan adawa yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben.
Shugaba Edgar Lungu ya tabbatar da mutuwar magoya bayan su biyu, indai ya ce kuma an yi na farko an yi na karshe, ko da yake hukumar zabe ta bada umarnin gudanar da bincike kan Musababbin hallaka mutanen biyu.
Yanzu haka Shugaba Edgar Lungu na son zarcewa ne a wa’adi na biyu, indai fafatawa tsakaninsa da dan adawa Hakainde Hichilema ta fi zafi, wanda kuma ya yi takara har sau biyar ba tare da yin galaba ba.