By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasar Nijar, Mohammed Bazoum, ya bayyana godiyarsa ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari bisa amincewa da aikin gina titin jirgin kasa daga Kano-Katsina zuwa Maradi na dala biliyan 1.96.
DUBA WANNAN LABARIN: Hadin Kai Da Hakuri Shine Mabudin Zaman Lafiya – Osinbajo
Shugaban na Nijar, wanda ya kai ziyarar aiki Najeriya, ya yi wannan yabon ne bayan wata ganawar sirri da suka yi da Buhari a fadar shugaban kasa ta Villa da ke Abuja ranar Laraba.
A watan Fabrairun shekarar 2021 ne dai shugaba Buhari ya kaddamar da aikin shimfida layin dogo na tsawon kilomita 284 daga Kano –Dutse – Katsina – Maradi wanda ya hada Kano a Najeriya zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar.
Aikin wanda Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta amince da shi a watan Satumbar shekarar 2020, an yi imanin cewa yana da matukar muhimmanci ga bunkasa harkar sufurin jiragen kasa a Najeriya da kuma yankin yammacin Afirka.
Aikin wada Mota-Engil Group, injiniyan ƙasa da ƙasa, da kamfanin gine-gine ne ke aiwatar da shi.
Kazalika aikin wanda zai samar da tashoshi 15 a kan hanyar, zai bunkasa harkokin tattalin arziki a jihohin Kano, Katsina, da Jigawa a Najeriya, da kuma Maradi a Jamhuriyar Nijar.
Bazoum ya ce, “Akan harkokin tattalin arziki, mun tattauna aikin layin dogo na Kano-Katsina-Maradi, kuma wannan aikin wani ababen more rayuwa ne da zai hade tattalin arzikin Najeriya da Nijar.
Don haka, na zo nan ne don in gode wa Shugaba Buhari bisa kokarin da ya yi na ganin cewa wannan aiki ya tashi, kuma ina fatan za a dore saboda wannan aiki zai kawo sauyi sosai a harkar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Mun kuma yi magana game da bututun iskar gas ta fuskar cewa iskar gas da mai a yanzu sun zama batu a siyasar duniya, da tattalin arzikin duniya.”
Ya kuma yabawa Najeriya kan yadda ta jagoranci gudanar da ayyukan rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa da ke kula da harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi.
“Ziyarar ta zo dai-dai da gagarumin farmakin da ake yi tare a hadin gwiwa a yau a yankin tafkin Chadi na yaki da ‘yan ta’adda, kuma wannan gagarumin farmakin na MNJTF ne – rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa.
Kuma kamar yadda kuka sani sarai, ayyukan rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa, kusan Najeriya ce ke daukar nauyin gudanar da ayyukanta. Kuma wannan aiki na nufin taimakawa wajen samar da kalubalen tsaro da kasashen mu biyu ke fuskanta.
“Ina so in sake jaddada shawarata da godiya ga Shugaba Buhari, wanda saboda goyon bayansa, wannan aiki yana gudana kuma za a ci gaba da aiki sosai a nan gaba,” in ji shi.
Shugaban na Nijar ya bayyana fatansa na ganin Najeriya da Jamhuriyar Nijar za su ci gaba da inganta alakar da ke tsakaninsu ta fuskar tsaro da ci gaban tattalin arziki.
An tattaro cewa shugaban na Nijar da ya kai ziyara ya samu liyafar cin abincin rana da Buhari ya yi masa jim kadan bayan ganawar tasu.
NAN