Shugaban Majalisar dattijai Ahmad Lawan ya yi maraba da nuna farin cikinsa na dawowar Sanata Orji Uzor Kalu mai wakiltar Abia ta Arewa majalisar.
Kalu dai rabonsa da majalisar tun Disambar shekara ta 2019, amma daga karshe dai ya samu dawowa majalisar a yau talata.
A yayin da yake masa maraba da zuwa Lawan yace “muna murna da dawowar dan uwanmun kuma babban jagora a majalisarmu”.
Cikakken rahoto na nan tafe………