A ƙalla yan yiwa kasa hidima sama da dubu biyu da dari biyar ne suka gudanar da zanga-zanga a Jihar Anambra don nuna adawarsu da dakatar da aikin yiwa kasa hidimar.
Kazalika masu zanga-zangar sun nuna mubaya’ar su da kasancewar Kasarnan tsintsiya madaurin ki guda.
Matasan waɗanda suka fara yada zango a dandalin taro na platoon sun kai har zuwa ten platoon, tare da gabatar da tocilar dunkulewar kasarnan ga hukumar gudanarwar NYSC.
Ko-odinetan hukumar Birgediya Janar Mista Kehinde Aremu shi ya karbi tocilar a madadin Darakta Janar na hukumar Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim.
Matasan yayin zanga-zangar sun kuma rike kwalaye dake nuna adawarsu da soke aikin yiwa kasa hidimar ta NYSC.
Da yake jawabi, Oremu ya ce huukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba ganin ta yi duk mai yiwuwa don kasarnta ci gaba da dunkulewa guri guda.
Daya daga masu zanga-zangar nai suna Mista Kolawole Oladapo ya ce matasan sun fito wannan zanga-zanga ne don nuna irin yadda kasarnan ke bukatar ci gaba da zama gida.