Wani matashin ɗan Najeriya ya nunawa sauran mazaje yadda yakamata ace suna yabawa matan su a ranar murnar zagayowar ranar haihuwar su.
Wani bidiyo wanda wani mai amfani da sunan @nesta_surprise8 a manhajar TikTok ya sanya, ya nuna lokacin da matashiyar matar tasa ta fashe da kuka saboda irin ɗimbin kyaututtukan da mijin nata yayi mata.
KU KARANTA KUMA: Ƴan ta’addan ISWAP sun yi rabon tsofaffin kuɗi a Borno.
Matashin yayi amfani da tsaɓar kuɗi har dubu ɗari biyar aka jera su a gabanta sannan ya kuma siyo mata filawoyi masu kyau na dubu ɗari biyu. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Domin tabbatar da cewa tana da hanyar samun kuɗin shiga, sai ya siyo mata sababbin keke Napeb guda biyu.Ya kuma ƙara mata da sabuwar iPhone 14 da agogon lu’u lu’u cikin kyaututtukan.
Matashiyar ta ɗauki hoto a gaban sababbin keke Napep ɗin, yayin da mutane da dama a wajen yin sharhi suka yabawa mijin nata bisa wannan namijin ƙoƙarin da yayi.
Ku kalli bidiyon a nan
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
elikachunga23 ya rubuta:
“Zan cigaba da yiwa saura tafi har zuwa lokacin da nima za a yi min.” Na taya ki murna.”
Martha unusual ta rubuta:
“Ra’ayin siyo keke Napep ya burgeni saboda wannan zata riƙa samun kuɗin shiga duk sati.”
dotunmide ya rubuta:
“Wannan keken hannun jari ya zuba mata. Yayi dubara sosai.”
Anni gold ta rubuta:
“Wannan duk inda ake namiji to ya kai saboda ƙarawa da wannan keke Napep ɗin.”
Ta Bayyana Komai: Wata Shiga Da Wsta Amarya Tayi a Wajen Bikinta Ta Janyo Cece-Kuce
A wani labarin na daban kuma, shigar da wata amarya tayi a wajen biki ya janyo cece-kuce.
Wani ƙayataccen bidiyo da aka sanya a yanar gizo ya nuna wani ango cikin ƙasaita yana nuna tsantar ƙaunar da yake yiwa kyakkyawar amaryar sa.
A cikin bidiyon mai matuƙar ɗaukar hankali, amaryar ta tsaya a gaban mutane tana yin jawabinta, yayin da angon na ta ya fito yana nuna matuƙar burge shi da tayi.