Hausawa dai suka ce kwana 99 ta barawo, kwana daya kuma ta mai kaya, kazalika kuma aka ce kumatun da zai sha mari, to lallai ba ya jin kwaɓa.
Wannan karin maganar tamu ta zo ne daidai lokacin da aka yi rashin Sa’a wata mata dake cin amanar mijinta ta tura wani sako na soyayya wa danta a madadin turawa wa dadironta.
A wani hoton fuskar waya wato screenshot da aka baza shi a yanar gizo bayan tura sakon a shafin WhatsApp, matar wacce aka gaza bayyana sunanta, ta tura wa ɗan nata ne sako tana sanarda shi cewa mai gidanta ya yi tafiya don haka lokaci ya yi sa za su sheke ayarsu ba tare da shamaki ba.
Ko da yake ta yi niyyar tura wa dadiron nata ne sakon, to amma bisa ga dukkan alamu dai ta sun jima suna wannan sheke aya, domin cikin sakon ta bayyana irin yadda take cewa wannan karon a cikin gida za su hole.
Ganin sakon ke da wuya ne dai dan nata hankalin shi ya tashi, inda ya nuna mata cewa lallai bata da godiyar Allah duk da irin kulawa da ubanshi wato mijin nata kenan ke yi mata.
Kuma dukda cewa ta gargade shi tare da alkawarin tukwici mai girma kan kada ya yaɗa labarin, daga baya dai an rasa ya aka yi labarin ya buwayi duniya.