Babbar majistaren dake zama a birnin Akure, babban birnin jihar Ondo, ta bayar da umurnin sakaya wani dattijo mai shekara 60, Samuel Gbadamosi, a gidan gyaran hali bisa zargin yiwa wata ƴar shekara 16 fyaɗe
Wanda ake ƙarar ya aikata laifin ne a gidan sa dake kan titin Obasekola, cikin ƙaramar hukumar Owo ta jihar. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Allah sarki rayuwa: Amarya ta rasu kwana 11 bayan aurenta
Jami’an ɗan sanda mai shigar da ƙara, Augustine Omhenemhen, ya gayawa kotu cewa wanda ake ƙarar ya yiwa yarinyar ta ƙarfi ne lokacin da tazo amsar littafi a wajen ɗiyar sa, wacce ƙawarta ce.
Wanda yake ƙarar yace laifin da ya aika ya saɓa sannan ya cancanci hukunci a kundin tsarin dokar jihar.
Sai dai wansa ake ƙarar yace bai aikata laifin ba, inda yace ba ta ƙarfi ya yiwa yarinyar ba. Ya kuma ƙara da cewa yarinyar da kanta ta yarda ya kwanta da ita ba tare da ya tilasta mata ba.
“Ban yi mata ta ƙarfi ba, dukkanmu mun amince da mu yi jima’i” A cewae sa.
Mai shigar da ƙarar ya nemi kotu da fa sakaya wanda ake ƙarar a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da babban ofishin jami’an shigar da ƙorafe-ƙorafe zai yi magana akan lamarin.
Lauyan wanda ake ƙarar, P.A Amuluru, ya roƙi kotu da tayi sassauci a hukuncinta, inda yayi alƙawarin kawo ƙwararan shaidu da waɗanda za su tsaya masa.
Da take zartar da hukuncinta, Majistare O.R Yakubu, ta bayar da umurnin a tsare wanda ake ƙarar a gidan gyaran hali na Olokuta har zuwa lokacin da ofishin DPP zai bayar da shawara akai.
Ta ɗage shari’ar har sai zuwa ranar 27 ga watan Afrilun 2023.
Bidiyo: Yadda Wata Amarya Ta Kama Ango Da Duka Ana Tsaka Da Biki
A wani labarin na daban kuma, wata amarya ta kama kilar angonta ana tsaka da biki.
An samu hargitsi a wajen wani bikin aure bayan kwatsam kawai amarya ta kama dukan ango a wajen bikin su a ƙasar Rwanda.
Bidiyon da aka ɗauka a wajen bikin ya nuna lokacin da ango da amarya suka fito daga wani katafaren gida suka nufi coci domin a ɗaura aure.