.
Daga Mukhtar Yakubu Kano
Fitaccen Mawaki kuma wanda ya ke gabatar da shirin Zafafa 10 a gidan talbijin na Arewa 24, Aminu Abba Umar Ringim ya bayyana wakokin su na HIP-HOP da cewar, wakoki ne da su ke koyar da tarbiyya da kuma samar wa da Matasa aikin yi.
Mawakin ya bayyana hakan ne a lokacin da wakilin jaridar Dimokuradiyya, ya ke yi masa tambaya a game da, yadda a ke kallon wakokin Hip-hop, a matsayin wakokin da su ke kawo gurbacewar tarbiyyar matsala, musamman ta bangaren kayan da su ke saka wa da kuma Raye-rayen da su ke yi.
Inda ya ke cewa “To ni ban yarda gaskiya wakokin Hip-hop suna lalata tarbiyyar Matasa ba, domin idan ka kula ni Mawakin hip hop ne, kuma ganin yadda wakokin su ke da tasiri a cikin Hausawa, a matsayina na Bahaushe, da na ke gabatar da shirin Zafafa 10 a gidan talbijin na Arewa 24, ai ina tsaftace harkar. Abin ma da na ke yi ina kokari ina datse duk abu na rashin kyautata wa da zai shigo.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamu kwato wa APC Yancin su
Ya kara da cewa, “Za ka ji ma ina maganar cewa, ba na son kaza. Ka ga idan kana son ka yi dole ka bi abin da muka tsara.” Inji shi.
“Sannan na biyu duk wani abu na nishadantar wa daga fim ne, waka ne, da ma ko menene, za ka ji an ce tarbiyyar jama’a a ke lalata wa, bayan kuma mutane sun sani baiwa ce.” A cewar shi.
“Amma ana son a dakusar da kai kana da hanyar da ka ke cin abinci, har ma kana taimakon wasu, don haka mutane su kula wakokin da mu ke yi na fadakarwa ne, ba na lalata tarbiyyar Matasa ba, kuma mu Hausawa ne Musulmi, idan an ga mun yi wani abu ba dai-dai ba, yana da kyau a jawo hankalin mu a gyara mana, ba wai a ce muna lalata tarbiyyar Matasa ba.”
A karshe ya ce “Don haka ina kira ga Jama’a da su sani wakokin da mu ke yi na hip hop sana’ar mu ce, kuma a ciki mu ke fadakar da jama’a, abin da ya kamata su yi, da kuma abin da za su kauce masa.” Kamar yadda Nomiis Gee ya bayyana.