- Wani daga cikin iyalan gidan Sarkin Kajuru, ya bayyana yadda ta kaya tsakaninsu da yan bindiga, wadanda suka sace Sarkinsu
- Ya bayyana cewa, yan bindigar sun nemi yafiyar iyalan masarautar
- Haka zalika, ya ce, yan bindigar sun bayyana cewa basu samu kwanciyar hankali ba tun bayan sace basaraken
Wani daga cikin iyalan gidan basaraken Kajuru, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya labarta yadda haduwarsu ta kasance da yan bindiga, wadanda sace Alhaji Alhassan Adamu, Sarkin Kajuru, a ranar Lahadi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda wasu masu dauke da muggan makamai suka yi awon gaba da sarkin tare da mutane 13 daga iyalansa, a cikin farfajiyar gidansa a ranar Lahadi.
Sai dai, a ranar Litinin ne aka saki basaraken yayin da sauran iyalan ke ci gaba da kasancewa a tsare a hannun yan bindigar, kamar yadda jaridar ta ruwaito.
Wata majiya, daga cikin wadanda suka je taryar sarkin, ya shaida cewa yan bindigar sun bukaci yafiyar yan uwa da iyalan masarautar kafin suka mika masu basaraken mai shekaru 85.
KARANTA WANNAN: Sabbin jami’ai: Rundunar sojin ruwa ta karyata labarin sunaye na Musamman, ta yi gargadi
Majiyar, wanda ya ke daga cikin wadanda suka taryin Sarkin Kajuru, ya ce yan bindigar sun kira su ne ta hanyar amfani da wayar Sarkin jim kadan bayan Sallar La’asar, kuma suka bukace su da su shirya taryar sa.
A wani labarin makamancin wannan, Tsohon Shugaban Kungiyar Yan jaridu ta kasa dake Kaduna kuma mazaunin garin Ibrahim Inuwa Kajuru , ya tabbatar wa da Gidan Talbijin na Trust Tv cewa Sarkin ya yi Magana da Mabiya sa a fadar shi dake garin Kajuru” a cewar shi.
Sai dai haryanzu ba’a tabbatar, ko an bai wa yan bindigan kudin fansa ba, kafin sakin Sarkin, amma dai tun da fari, sun bukaci a ba su Naira milliyan dari biyu, kafin sakin Basaraken Mai shekara 85.
Haka zalika, al’ummar garin Kajuru sun yi cikar dangon fari a ranar Litinin domin murnar dawowar Sarkin su.
Da misalin karfe 5:25 na yammaci ne aka saki Sarkin, inda mazauna garin suka yi dandazo a fadarsa domin murnar dawowarsa.
Comments 1