Wani Mutum ya makale a wata katafariyar gada a kasar China inda yake ta bilunbituwa a kai bayan da iska ta kakkarya gilasan ta.
Mutumin yana yawon shakatawa ne a kan gadar mai tsawon murabba’i 100, daidai da kafa 330 kenan sa’ilin da ibtila’in ya faru a tsaunin Piyan.
Saboda karfin iskar, sai da aka ga yadda ɓurbushin gilasan na shawagi a sararin samaniya, Inda wasun su suka yi nisan kilomita 150 cikin Sa’a guda.
Kasar ta China a yanzu haka an yi kiyasin cewa tana da gadojin gilasai sama da 2300 tare da hanyar masu tafiya a kafa.
An gina gadojin ne da zummar jawo hankalin masu yawon shakatawa da yan jari hujja don bunkasa harkokin yawon bude idon kasar.
Wani faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna yadda mutumin ke ta bilunbituwa tare da kara kaina a tsakiyar gadar dake birnin Longjing.
Yan Kwana-kwana sun yi gaggauta kai mishi doki inda suka yi nasarar ceto shi tare da garzaywa da shi asibiti don duba lafiyarsa.