Wani matashi ɗan Najeriya mai suna @willchukz, yayi wani ɗan gajeran bidiyo domin nunawa mutane masoyiyar sa yayin da yake rera waƙar dake fitowa daga abin sautin motar sa.
Matashin ya haska kyamarar sa zuwa wajen da wata tsohuwar baturiya take wacce ke zaune a kusa da shi tana yi masa murmushi. Jaridar Legit.ng ta rahoto
KU KARANTA KUMA: Batun dakatar da Opay da Palmpay, CBN ya bayyana gaskiyar zance
Yanayin da matashin yake ciki ya nuna cewa yana matuƙar farin ciki da samun wannan masoyiyar ta sa.
Mutane da yawa waɗanda suka yi sharhi akan bidiyon sa na ta maganar samun sa’ar su ma su yi wuff da wata baturiya, inda wasu suke nuna cewa shi fa kakar sa ta riga da ta gama yanke saƙa.
Akwai wata budurwa wacce cikin raha tayi fatan kada wata baturiya tayi wuff da mijin da zata aura.
Bidiyon ya yaɗu sosai inda sama da mutum 200 suka yi sharhi akan sa, yayin da sama da mutum 14,000 suka danna masa alamar ‘like’
Ku kalli bidiyon a nan
Ga kaɗan daga cikin waɗanda Dimokuraɗiyya ta tattaro:
@Nobodycares ya rubuta:
“Kai da abin ya zo kanka sai ka ɗauko ƴar’uwar Elon Musk ka kawo inda Evian take.”
Malaga ya rubuta:
“Waɗannan yaran Benin ɗin kun fara ko.”
@tinanice04 ta rubuta:
“Kada wata baturiya taje ta aure min mijin da zan aura fa ooo.”
@Therejectedston said:
“Duk waɗannan yaran Benin ɗin kun cika zaƙewa.”
“Dan Guntun Gatarinka” Wata Mata Ta Koma Gidanta Da Ba a Kammala Ba, Mutane Sun Yaba Mata
A wani labarin na daban kuma, wata mata ta sha yabo sosai bayan ta koma gidan ta wanda ba a kammala ba da zama
Wata mata mai suna @shantellebelle, wacce ta ƙudiri aniyar cin ƙashin gashin kanta ta tattara kayanta ta koma gidanta duk da ba a kammala ginin sa ba.
A wani bidiyo da aka sanya a TikTok, matar ta nuna gadon da ta sanya a tsakiyar gidan domin ta riƙa barci. Ta bayyana cewa a haka kawai zata riƙa kwanciya a kansa.