Wasu ya bindiga sun kutsa masallaci a garin Jibiya na Jihar Katsina yayin da ake tsaka da Sallar Tahajjud inda suka yi awon gaba da mutane sha biyu a daren jiya.
Wani Mazaunin garin Mallam Fahad Mukhtar ya tabbatar da aukuwa wannan mummanan labari ga manema labarai da sanyin safiyar yau.
Ya ce yan bindigar sun kutsa ne wuraren karfe 2 na dare inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi, kafin daga bisani bayan sun firgita jama’a sai suka kwashi mutane sha biyun.
Ko da yake da ma tun da farko sai da aka gargadi jama’a kan barazanar hari daga yan bindiga, kamar yadda Mallam Fahad ya bayyana.
“Kafin zuwan su, sai da aka yi ta yadawa a shafin sada zumunta na WhatsApp, cewa akwai yiwuwar fa wasu bata gari za su shigo wuraren 12 na dare”
Mu dai addu’ar mu a nan ita ce, Allah Ya kawo mana dauki da mafita a garin Jibiya, Yanzu hare-hare ake yi ba dare ba rana” Cewarsa.