Daliban makaranta uku, ‘yan uwan juna, ana fargabar sun mutu lokacin da motar jigilar Fasinjoji ta bi ta kan su a babbar hanyar Kajola/Igbominasi da ke Ilesa na Jihar Osun a safiyar yau Litinin.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nigeria (NAN) ya ba da rahoton cewa, ‘yan uwan sun gamu da ajalinsu ne a kan hanyarsu ta zuwa makaranta.
Don haka mazauna yankin sun toshe babbar hanyar don nuna rashin amincewarsu da yadda masu ababen hawa ke gudun wuce kina.
Toshewar ta haifar da toshewar hanyar da ta tilasta masu motoci su nemi wasu hanyoyi.
KARANTA WANNAN LABARIN: EFCC ta yi Awon Gaba da Shugaban KAPSUDA na jihar Kaduna
Wani ganau ya shaidawa majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa, wata Mota kirar bas, ta ci karo da daliban yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa makaranta sannan aka garzaya da su asibiti kafin ‘yan sandan su isa wurin da lamarin ya afku.
“‘Yan sanda sun kuma ja motar bas din,’ ‘in ji shi.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar Osun, SP Yemisi Opalola, ta tabbatar da faruwar lamarin sannan ta ce, yan sanda sun San halin da ake ciki a yankin, Kuma suna bakin kokarin don dawo da zaman lafiya a yankin.
Kazalika ta kara da cewa, za a kuma bayar da cikakkun bayanai game da hatsarin nan ba da jimawa ba.
Comments 2