• Hukumar kula da kafafen sadarwa na Kasa NCC, ta ce Kamfanin Airtel bai sabunta Lasisin shi ba.
• Tun da fari dai, Babban Daraktan Kamafanin Airtel a Nigeria ne ya fara cewa, kamfanin ya sabunta lasisin shi har na tsawon shekaru Goma masu zuwa.
• Sai dai a wata sanarwa da Daraktan kula da harkokin al’uma na yau da kullun a hukumar NCC Adinde ya fitar a jiya Lahadi, ta karyata bayanin kamfanin Airtel.
Hukumar Kula da kamfanin sadarwa ta kasa NCC ta ce, har yanzu kamfanin sadarwa na Airtel bai sabunta lasisin gudanar da aiki shi ba a kasar nan.
Daraktan kula da harkokin jama’a na hukumar ta NCC Dakta Ikechukwu Adinde ne, ya bayyana hakan ga mane ma labarai a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi, a bababn birnin tarayya Abuja.
.
A cewar shi, an janyo hankalin hukumar ta NCC, kan wani bayanin ta yanar gizo da Babban Daraktan Kamfanin Sadarwa na Airtel a Nigeria, Mr Segun Ogunsanya ya wallafa, na cewa, kamfanin Airtel din ya sabunta lasisin gudanar da aikin shi a Nigeria, har na tsawon shekaru 10 masu zuwa, a nan gaba.
Mr Ogunsanya ya bayyana hakan ne a jihar Legas a ranar 14 ga watan Yulin Shekarar 2021, lokacin da ya ke yi wa kafafen yada labarai bayani kan sabon shirin Kamfanin na Airtel, na Bunkasa wal-walar al’uma mai taken “Touching Lives Season 6”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Harin Yan bindiga: Yan sanda 13 sun bakunci lahira a Zamfara, da wasu Mutum uku
A nashi mangaren Adinde ya bayyana cewa, Kamfanin Airtel ya bukaci sabunta Lasisin gudanar da aiyukan shi a Nigeria na UASL, da Hukumar kula da kafafen sadarwa ta kasa, Amma haryanzu, Kamfanin bai sami amince wa daga hukumar ta NCC ba, inda ya ce, lamarin na bukatar bin wasu ka’idoji.
Kamfanin Dillancin labaran kasar nan NAN ya ruwaito cewa, lokacin kaddamar da shirin na Kamfanin Airtel a ranar Laraba a garin Legas, Mr Ogunsanya ya ce, Airtel ya sabunta lasisin shi a yunkurin kamfanin na bungakasa, da tallafawa al’umar ta hanya mai amfani, da kuma dorewar amfanuwar al’uma.
Comments 1