Wata budurwa ta wallafa gajeren bidiyonta wanda ta sanya karenta cikin shayin bayan kai shi wurin budurwarsa a makwabtansu, Legit.ng ta ruwaito.
Yayin da ta mika shi wurin karyar, nan da nan su ka fuskanci juna cike da shauki, wanda wannan bidiyon yayi matukar daukar hankalin jama’a.
KU KARANTA: Budurwa ta sharara wa saurayinta mari, ta ƙi amsar tayin aurensa, ta buƙaci ya zage damtse
Budurwar mai suna @itemeleng_belinda, ta bayyana had da ta bar karenta ya je inda yake so da kansa.
Bayan sakanni ke dan a cikin bidiyon sai ta gane cewa wurin budurwarsa yake son zuwa. Karnukan sun kamu da soyayya juna, dukkan alamu na nuna hakan.
Kuma makwabtan juna ne wanda hakan yasa aka gane cewa soyayya su ke yi.
A lokacin da su ka ga juna sai su ka shiga shauki da farinciki mara misaltuwa. Sun ci gaba da matsawa kusa da juna don nuna kusancin su.
Karen budurwar bai so barin wurin ba bayan haduwarsa da abar kaunarsa.
Saurayina Yana Bani Sama da Miliyan N11m Duk Wata Don Gyara Kaina, Budurwa
Wata yar Najeriya mai suna Okuneye Idris Olarenwaju wanda aka fi sani da Bobribsky ta tayar da hazo a dukkanin kafafen sada zumunta a yayin da take fadi game da abinda saurayin nata yake bata, gospelarea.com ta rawaito.
Bobribsky, ‘yar shekara 31 da haihuwa, ta wallafa ta shafinta na sada zumunta na Instagram kuma ta tambayi mutane nawa ne kudin da saurayinsu ke ba su a matsayin kudin ciyarwa a kowane wata.
Bayan haka, ta bayyana cewa saurayin nata yana ba ta dala 7000 duk wata don ciyarwa, sannan kuma yana bata kudin gyaran gashi dala 5000 duk wata.
Kazalika ta kara da cewa yana bata kudin siyan man fetur da siyayyar sauran kayayyaki, wanda ya kai dala 5000 duk wata.