Labarin Wata baturiya yar kasar Austiraliya a wannan makon na daga cikin manyan labarai da suka karade shafukan sada zumunta na intanet inda ta ce harshen ta ya sauya bayan da aka yi mata yiyata a makogoro.
An yi wa matar mai suna Angela Yen ne yar shekara 27 aiki a ranar 19 ga watan Afirelun da ya gabata, inda kwanaki goma bayan aikin ne sai harshen ta na Aussie ya koma na kasar Jamhuriyyar Ireland.
“Ban taɓa zuwa kasar Ireland ba, a nan Austaraliya na yi girma tun bayan da muka dawo nan din shekara ashirin da suka gabata lokacin ina ywr shekara bakwai.”
A yanzu haka matar ta sake komawa ga likitocin da suka yi mata wannan aiki don gano menene Musababbin sauyuwar harshen nata.
To sai dai wani likita mai suna Karl Kuszelnicki ya ce wata kila matar na da ruwa biyu ne ta inda za ta iya yarurrukan kasashen waje.
Ya ce binciken da aka gudanar ya gano cewa mutum ka iya magana tamkar dan wata kasa, kuma hakan na faruwa ne sakamakon wata matsala ta Ƙwaƙwalw da mutum ke gama da shi, to sai dai Yen ta ce ba ta da wata matsalar Ƙwaƙwalwa.