Wata hira tsakanin saurayi da budurwa ta kacame inda saurayin ya rabu da budurwarsa kan ta yi masa miya da bagen tumatur kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Matashi ya tura budurwarsa kasuwa inda ya bukaci ta yi cefanen kayan miya wanda bayan ta dawo ta gane cewa cikin tumaturan akwai lalatacce.
KU KARANTA: Saurayina yana bani sama da N11m duk wata don gyara kaina, Budurwa
Saidai a haka ta hada da shi tayi miyar wanda saurayin nata bai nuna damuwarsa ba inda ya dinga tunanin cewa ko an yi miyar ba za ta shafi dadin abincin ga.
Saidai bayan an kammala abincin budurwar ta ki ci, ta nace cewa saidai saurayin ya ci shi daya.
Wannan lamarin ya sanya saurayin ya hassala inda ya fara sauya ra’ayi dangane da soyayyar da yake mata.
Matashin ya zauna ya yi mata bayani dalla-dalla inda ya fara da cewa:
“Na ba ki kudina don ki je ki yi cefane ki siyo kayan-miya. Kin dawo kin yayyanka tumatur din har da mara kyau a ciki. Mun kula da hakan kuma na yi tunanin idan an soya miyar ba za a gane ba.
“Yayin da ki ka soya sai ki ka zuba min ni daya. Babu yadda ban yi da ke ba amma ki ka ce ni kadai zan ci, ke ba kya jin yunwa. Na yi juyin duniya dake kan ki ci ko cokali daya ne amma ki ka ki duk da tun safe rabonki da abinci.
“Kuma a lokacin ki ka ce ba za ki iya ci ba saboda akwai lalataccen tumatur. Kin san be dace a ci ba amma ki ka girka ki ka bani? Meyasa ki ka girka min a haka?”
Budurwa ta tashi saurayi a Twitter bayan ya ce ya shirya aure amma babu matar aure
Wata mata a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba ta tashi wani matashi a Twitter yayin da ya bayyana cewa yana da zone amma bai samu budurwar da zai nemi aurenta ba, LIB ta ruwaito.
Abin ya fara ne bayan wani kwararre a harkar soyayya ya bukaci wadanda su ka yi aure da su gabatar da hotunan aurensu.
Sai dai matashin ya wallafa hoton zobe a hannunsa inda yace na aure ne amma har yanzu be samu matar da zai aura ba.