A safiyar Larabar nan ne ‘yan Najeriya suka wayi gari da ganin da hotunan yan kungiyar kwallon kafa ta mata ‘yan kasa da shekaru 20 a cikin mawuyacin hali.
Jaridar Dimokradiyya ta rawaito yadda yan wasan hotunan su cikin yanayi na tsilla tsilla suka karade shafuka Internet.
Yanzu haka dai yan wasan na cikin yanayi na gararanba a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.
Tawagar Falconets dai na kan hanyar komawa Najeriya ne bayan ficewarsu daga gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 20 a kasar Costa Rica.
KARANTA ANAN: Kungiyar NAPTAN Ta Nemi Bayar Da Gudunmawar 10,000 Don Magance Matsalolin ASUU
Bayanai sun ce ‘yan matan sun tashi daga otal dinsu da ke Costa Rica da karfe 6:30 na safe agogon kasar tun a ranar Litinin, kuma an ba su takardar izinin tafiya ta Colombia zuwa Istanbul zuwa Abuja.
Toh Sai dai kash, jirgin Turkish Air ya jinkirta tashi daga Colombia zuwa Turkiyya na tsawon sa’o’i 2 da mintuna 30 wanda hakan ya sa suka rasa jirgin da zai kai su zuwa Turkiyya.
Hakan ya sa suma suka rasa jirgin da zai kawo su Abuja daga Turkiyya.
Jami’an hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) karkashin jagorancin Ruth David sun roki mahukuntan filin jirgin da su bar yan kungiyar su samu masaukin otal amma sun dage cewa tunda kungiyar ba ta da bizar wuce gona da iri, ba za a bar ‘yan wasan su shiga ba, sae dai su fice daga kasar kai tsaye daga filin jirgin.
Falconets ta lashe dukkan wasannin rukuni uku na rukunin C don samun maki 9 mafi girma amma bajintar da suka yi ta daina aiki a wasan daf da na kusa da karshe lokacin da Netherlands ta doke su da ci 2-0.
A wani labarin kuma:
Amurka Ta Rattaba Hannu Da Najeriya Kan Wata Yarjejeniyar Mayar Da $23