Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun tare hanyar Katsina zuwa Jibia a ranar Laraba inda suka yi garkuwa da wasu matafiya da ba a tantance adadinsu ba. Wani shaidar gani da ido ya ce an kai harin ne da misalin karfe 5 na yamma a kauyen Kadobe.kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Wata Majiyar ta ce ‘yan bindigar da suka zo a kan babura kusan shida, sun mamaye titin tare da harbe harben bindiga don tsoratar da fasinjoji kafin su yi awon gaba da mutanen da ke cikin motoci biyu.
“Ba su fi 20 ba saboda sun zo a kan babura kusan shida ne. Ba su yi amfani da wani shingen hanya ba sai dai sun tsaya a kan titin da bindigoginsu suka fara harbi ta sama. Hakan ya sa biyu daga cikin Direbobin motocin suka rasa shawo kan motocin inda suka kauce kan titin kuma a karshe ‘yan bindigar sun yi awon gaba da mutanen,” inji shi..
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben 2023: Yankin Arewa Maso Yamma Nada Matukar Mahimmanci Ga Nasarar APC – Dattijo
Shaidan ya yi zargin cewa an sanar da jami’an tsaro game da farmakin ne bayan mintuna 30 da barin maharan.
Majaiyar Dimokiradiyya ta ruwaito cewa, a baya-bayan nan ‘yan bindiga sun sha kai hare-hare kan hanyar Katsina zuwa Jibia duk da shingayen binciken jami’an tsaro da kuma barikin sojoji da ke kan hanyar.
Sai majiyar ta ce, Ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah ba domin tabbatar da faruwar lamarin har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton saboda bai amsa kiran da aka yi masa ba.