Dan takarar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Alh Muhammad Sani Dattijo, ya ce shiyyar Arewa maso Yamma na da matukar muhimmanci ga nasarar jam’iyyar a 2023. Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito
A cewarsa, a shekarar 2015 jimillar kuri’un da aka kada wa APC (Shugaba Buhari) ya kai kashi 46%, yayin da a shekarar 2019 yawan kuri’un da aka kada ya ragu zuwa kashi 39%.
Dattijo, wanda tsohon shugaban ma’aikata ne a gidan gwamnatin Kaduna, ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso yamma da aka gudanar a Kaduna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Hukumar EFCC Ta Kama Akantan Hukumar NDDC Kan Badakalar Naira Billiyan 25
Ya bayyana cewa maimaita irin wannan nasarar da jam’iyyar ta samu a 2023 na nufin Arewa maso Yamma na da matukar muhimmanci ga nasarar APC azaben 2023.
“Arewa maso yamma ne ke da alhakin nasarar APC a zaben da ya gabata saboda Arewa maso yamma na da matukar muhimmanci ga nasarar APC.,” inji shi.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar Think Nigeria Group, Alh Nasiru Ladan, ya bayyana cewa bai kamata batun yanki ko addini ya zama ma’auni na auna ’yan takara ba, a’a, a auna tarihinsu.
Ya ce da zarar Najeriya ta daidaita, tafiyar kasar zuwa daukaka ta tabbata.
Tun da farko, shugaban kungiyar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ta kasa, wadanda suka shirya taron, Abdullahi Aliyu Katsina, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin ‘ya’yan jam’iyyar na shiyyar da kada su yi kasa a gwiwa wajen ganin APC ta ci gaba da kasancewa jam’iyyar da za ta iya doke su a zaben badi.
Ya bayyana kwarin guiwar nasarar jam’iyyar a 2023, ya kuma shawarci duk wata kungiya mai goyon baya a shiyyar da su yi aiki tukuru domin jam’iyyar ta ci gaba da rike madafun iko.