Rahotanni na nuna cewa, Yan bindiga sun yi garkuwa da Matar Dan majalissa Mai wakiltar bazabar Bakori dake jihar Katsina Dakta Ibrahim Kurami tare da Yayan shi biyu.
A cewar wani mazaunin yankin ya ce Yan bindigan sun afka gidan Dan majalissar ne dake kauyen Kurami na karamar Hukumar Bakori da musalin karfe 9 na daran jiya Asabar bayan sallahr Isha’i.
Kazalika masaunin yankin wanda ya bukaci a sakaye sunan shi ya bayyana cewa, yan bindigan sun fara farmakan yan agajin addin musulumci kafin su afka kauyen.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bercelona ta ce ba bu babun Korar Koeman, Lukako ya yabawa inter Milan
Mazaunin Wanda Shima ya sami rauni sanadiyar harin, an yi gaggawar kai shi wani cibiyar kiwon lafiya, domin kula da lafiyar shi.
A kawo yanzu ya yin hada wannan rahoto Dan majalissar Dokokin yana wurin taro Gaggamin jam’iyar APC na karamar hukumar sa.
Mai Magana da yawun rundunar yan sanda jihar Katsina SP Gambo Isah a ya yin tattaunawar shi da Tashar talbijin na Channels ta wayar salula ya ce, zai ce Wani abu kan lamarin, da zaran ya kammala samun bayanai daga jami’in dan sandan dake kula da yankin Bakori kan harin