Wasu yan kungiyar Inyamurai ta IPOB sun yi awun gaba da wani jami’in dan sanda a garin Nnewi dake Jihar Anambra.
Wannan lamari ya faru ne a gaban cocin Cathedral dake garin na Nnewi yayin da kuma suka cinna wuta wa motar dan sandar.
Kawo yanzu dai ba a san ina jami’in dan sandar yake ba, sai dai shadun gani da ido sun bayyana cewa yan bindigar IPOB ne suka sace shi tare da bankawa motarsa wuta.
Jihar Anambra dai ta shiga halin ɗar-ɗar tun bayan da aka bayyana kisan Kwamandar Ƙungiyar Inyamurai ta IPOB Samuel Uzo Okoro wanda aka fi sani da Biggy.