Majalisar wakilai za ta dawo zamanta a ranar 20 ga Satumba, a zauren wucin gadi. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da magatakardar majalisar, Yahaya Danzaria, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamu Kashe Naira Billiyan 1.2 Domin Gyaran Wasu Hanyoyi—Gwamnatin Kano
Danzaria ya ce saboda gyaran da ake yi a tsohuwar zauren majalisar, ana sa ran mambobin za su koma zama a sabon dakin da aka gyara a sabon ginin mai dauke da kujeru 118 kacal.
Ya ce an fadada sabon dakin ne ta hanyar samar da bene mai kujeru 236, inda ya kara da cewa an hada dakunan da na gani da sauti da na’ura mai kwakwalwa da manyan allon Magiji.
Sai dai ya ce babu wasu kujeru da aka kebe baya ga kasafin shugabanni da manyan jami’ai, yana mai cewa duk sauran shirye-shiryen zama za a yi su ne nan gaba kadan.
“Hakazalika yana da mahimmanci a lura cewa saboda wannan tsari ne na wucin gadi da aka tsara ba wani tanadi da aka yi wa mataimakan majalisa saboda rashin sarari.
Majalisar a ranar 20 ga watan Yuli ta ci gaba da hutun watanni biyu gabanin zagayen karshe na zama na 9.
Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, a ranar 14 ga watan Satumba, ya yi kira da a gaggauta kammala aikin gyaran majalisar dokokin kasar, gabanin wa’adin mika mulki a watan Agustan 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutame Biyu Sun Mutu, Yayin Da Akasamu Barkewar Cutar Kwalara A Sansanin Tubabbun Mayakan Boko Haram
Akalla mutane biyu ne suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a wani wurin da tsaffin mayakan Boko Haram ke zaune a Maiduguri na jihar Borno.
An bayyama hakan ne ta bakin Zuwaira Gambo kwamishiniyar harkokin mata da cigaban al’umma ta jihar
Comments 1