A ranar Lahadi ne gwamnatin jihar Kano ta ce za ta kashe sama da Naira biliyan 1.2 wajen gina shataletale, gyara da kuma kula da wasu manyan tituna da suka lalace a jihar. Kamar yadda Punch ta ruwiato
Hakan ya biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya yi sanadiyar ambaliya a fadin jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cutar Kwalara Ta Barke a Sansanin Tubabbun ‘Yan Boko Haram, Ta Fara Kisa
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Malam Muhammad Garba, ya bayyana cewa da za agyara sun hada da na gidan Man A.A Rano da First Bank da dai sauransu, kuma an shirya sake gina su a wasu wuraren.
A cewarsa, an kafa wani kwamitin fasaha da ya kunshi injiniyoyi daga ma’aikatar ayyuka da samar da ababen more rayuwa, hukumar tsara birane da raya birane ta jiha da kuma wasu ma’aikatu da hukumomi domin nazarin lamarin don daukar matakin gaggawa.
Garba ya ce tuni kwamitin ya tuntubi kamfanonin da ke karbar kwangilar wadanda aka zaburar da wasu daga cikinsu domin gudanar da aikin.
Kwamishinan ya ce, an ware wasu guda takwas na tituna domin gyarawa da kuma kula da su da nufin tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa cikin sauki.
Ya ce wasu daga cikin hanyoyin sun hada da Audu Bako Way, Sani Marshal Road, Mission Road, Hotoro Tsamiyar Boka Road, Layin Kaura Goje, Sheikh Hassan-Layin Gidan Biredi-Sani Bello Road, Kwanar Jaba-Kwana Hudu zuwa kadar Gayawa Road Bridge.
Sauran sun hada da FCE-Kofar Famfo, Gwarzo Road, Sheikh Jafar Road, Muhammadu Buhari Road, New Hospital Road, Sabo Bakin Zuwo Road, Lamido Crescent,hanyar da ta Tunkari cibiyar Magance Cutar Kansa, Dakata Road, Babban hanyar DanHassa zuwa babban hanyar gabashin Kano, ‘Yan Mota-Kofar Mazugal, Abagana Street Fagge.
Kwamishinan ya kuma lissafa sauran hanyoyin da suka hada da Aminu Kano Way-Kofar Ruwa, Festing-Bompai, France Road, Igbo Road, Gwammaja-Wapa, Kurna Babban Layi, Madaki Street Yolawa, Sabon Titi Mandawari, Kwanar Dala-Gidan Malam Aminu. Junction, Lafiya Road.
Garba ya kuma bada jerin sunayen wasu hanyoyin da suka hada da Bello Terrace, Alu Avenue da Iyaka Road.
A WANI LABARI KUMA: Babu Abunda APC Ta Haifarwa Najeriya Banda Yunwa Da Talauci – Okowa
Gwamnan jihar Delta kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Dakta Ifeanyi Okowa, a jiya Asabar ya ce yunwa da fatara da ake fama da su a kasar nan na faruwa ne sakamakon rashin tafiyar da tattalin arzikin kasa da jam’iyyar APC mai mulki ta yi.
Ya bayyana hakan ne a wani shiri na karfafawa al’ummar mazabar Ika da dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar a majalisar wakilai, Mista Victor Nwokolo, a Boji-Boji Owa, karamar hukumar Ika ta Arewa maso Gabas.
Comments 2