.
Bayan sanarwar da Rasha ta fitar a jiya na cewa za ta tura dubunnan dakaru domin yaki a Ukraine, kakakin rundunar sojin Rasha ya ce tuni ‘yan kasar Rasha 10,000 suka ba da kansu da kansu a ranar farko ta fara yada wannan gangamin. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
“Kimanin ‘yan kasar 10,000 ne suka isa ofisoshin daukar Jami’an soji da kansu ba tare da jiran an kira su ba,” in ji Vladimir Tsimlyansky a cikin kalaman da kamfanin dillancin labaran Rasha Interfax ya nakalto.
KARANTA WANNAN LABARIN: Na Yi Alkawarin Ba Zan Bar Jam’iyyar PDP Ba, Amma..—– Wike
Sai dai kafar yada labarai ta BBC ta ce, ba zata iya tantance gaskiyar wannan adadin ba.
Sai dai Sama da masu zanga-zanga 1,300 ne aka tsare saboda zanga-zangar adawa da sanarwar gangamin tura wasu dakarun zuwa Ukraine domin cigaba da Yaki, tsakanin jiya Laraba zuwa yau, bisa ga sabon alkalumman da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Rasha OVD-Info ta fitar..
A WANI LABARIN KUMA: Yanzu-Yanzu: Gwamna Tambuwal Ya Zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya
Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto a yanzu shine shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), inda ya karbi ragamar gudanarwar daga hannun takwaransa na jihar Ekiti Kayode Fayemi.
“Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti Dr. John Kayode Fayemi a yau a wajen taron majalisar tattalin arzikin kasa da aka gudanar a fadar Aso Rock Villa dake Abuja ya mika ragamar gudanarwar ga gwamnan jihar Sokoto. Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal,” kakakin kungiyar Abdulrazak Bello-Barkindo ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis.