Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto a yanzu shine shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), inda ya karbi ragamar gudanarwar daga hannun takwaransa na jihar Ekiti Kayode Fayemi. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito
“Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti Dr. John Kayode Fayemi a yau a wajen taron majalisar tattalin arzikin kasa da aka gudanar a fadar Aso Rock Villa dake Abuja ya mika ragamar gudanarwar ga gwamnan jihar Sokoto. Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal,” kakakin kungiyar Abdulrazak Bello-Barkindo ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cin Hanci Da Rashawa Na Kara Rura Wutar Rashin Tsaro A Najeriya – ICPC
A cewarsa, Fayemi zai mika ragamar jagorancin kungiyar a Hukumance ga Tambuwal a ranar 16 ga Oktoba, 2022.
Abdulrazaque ya kara da cewa, “Gwamnan jihar Sokoto zai ci gaba da rike mukamin har zuwa watan Mayun shekara mai zuwa lokacin da za a gudanar da zaben wanda da ya dace a tsakanin gwamnonin Najeriya”
Har zuwa mukaminsa na baya-bayan nan, Gwamnan Sokoto shi ne Mataimakin Shugaban kungiyar. Kuma ya yi wannan aiki ne har na tsawon shekaru hudu.
A WANI LABARIN KUMA: Barazanar Tsaro Ta Sanya DSS Buƙatar ASUU Ta Janye Yajin Aiki
Hukumar jami’an tsaron farin kaya DSS ta bukaci kungiyar malaman jami’a ta kasa ASUU da ta janye yajin aikin da take yi saboda dalilan tsaro.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da kotun da’ar ma’aikata ta baiwa kungiyar malaman jami’ar umarnin janye aiki da suka shafe watanni bakwai suna yi saboda rashin cika musu alkawarukan su da gwamnatin tarayya tayi.