Dakarun Yan Sanda sun chafke mutane goma sha takwas bisa laifin hakar zinare ba bisa ka’ida ba a karamar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Wannan kamu ya biyo bayan umarni da Shugaban kasa ya bayar ne na hana hakar zinaren a jihar sakamakon yanayin tsaro.
Kakakin rundunar yan sandar Jihar SP Shehu Muhammad ya ce dakarun yan sanda dake yakki da hana hakar zinaren karkashin jagorancin SP Murtala Bello sun yi dirar mikiya a gurabe daban daban da ake hakar zinaren inda suka yi nasarar chafke wadannan mutane.
Daga cikin guraben a cewar Kakakin sun hada da garin Kwali dake karamar hukumar Bukkuyum da Daki Takwas dake karamar hukumar Gummi da Zugu da Wawan icce dukkaninsu su kuma dake ƙaramar hukumar Anka ta jihar.
Ya ce dakarun yan sandar sun bazama farautar marasa jin ne tun a watan Disambar bara inda sun yi nasarorin kawo karshen hakar Ma’adinai a girabe da dama tare da chafke masu kunnen kashi bila-adadin
Daga bisani ya ja kunnen duk wani mai kunnen kashi da ya shafa wa kan shi ruwa muddin yana son kan shi da lafiya.