• Nafisa ta ce haryanzu Ana samun kudi acikin masa’antar kannywood.
• Yanzu ba wahala mutun ya yi suna a harkar fim, ba kamar da ba.
• ko yanzu nasami mujin aure Wanda kesona tsakanin da Allah zanyi aure.
Tsohuwar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood Nafisa Ishak Rano, ta bayyana irin ci gaban da harkar fim ta samu a wannan lokacin, wanda ta ke ganin a yanzu ba sai an sha wahala ba, a ke yin suna a cikin harkar.
Jarumar ta fadi hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin mu, in da ta ke cewa “Duba da yadda harkar fim ta ke a yanzu, an samu ci gaba sosai ni a gani na, idan aka kwatanta yadda harkar take a baya,” Domin kuwa a cewar ta ” Na dade a cikin masana’antar tsawon shekaru sama da goma, kuma na yi fina-finai da dama har ma na zuba kudi na yi Furodusin, amma hakan ba ta sa na yi suna ba. Amma a yanzu idan ka duba ko ba ka saka kudi ka yi fim ba, to harkar fim ta yi bunkasar da duniya za ta san ka. ”
Ta ci gaba da cewar” Ka ga yanzu ina yin fim din Dadin Kowa, wanda a yanzu ta dalilin sa duniya ta sanni.
Ta kuma kara da cewa “ina yin wakoki wanda a ke sakawa a YouTube, wanda su ma ta dalilin wannan jama’a sun sanni sosai, don haka an fi samun daukaka a wannan lokacin fiye da lokacin baya. ” Inji ta
KARANTA WANNAN LABARIN: Alkalin Alkalai zai nada sabbin Alkalai 18 a gobe Litinin
Mun tambaye ta ko ba kya ganin a yanzu ana ganin kasuwancin fim din ya mutu ne shi ya sa aka koma gidajen TV da kuma YouTube?
Sai ta ce” Ai komai lokaci ne, don haka a yanzu ma ana samun kudi a fina-finan da a ke sakawa a YouTube din, kuma wanda a ke yi na Dadin Kowa ai shi ma ana biyan mu, don haka muna samun ci gaba sosai, harkar fim dai a yanzu sai godiyar Allah. ”
Ko wanne buri Nafisa Ishak Rano ta ke so ta cimma a cikin harkar fim nan gaba?
To ni dai buri na shi ne na gama harkar Lafiya na samu miji na yi aure. Domin ko yanzu na samu miji wanda yake so na domin Allah, sai na aure shi, domin aure shi ne darajar mace.”
Daga karshe ta yi kira ga masoyan ta da su taya ta da addu’a, domin ta samu ta gama da harkar fim Lafiya.
Comments 1