Labarin dake shigo mana a halin yanzu na nuni da cewa; gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu a ranar Juma’a ya sanya hannu a dokar karbar Haraji ta jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Gbenga Omotoso, shi ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya fitar a yau Juma’a, inda ya ce Gwamnan ya sanya hannu a dokar ne bayan da ya dawo ziyarar wani aiki da yaje.
Bayanin na cewa; “Gwamnan ya sanya hannu kan dokar sanyawa wadansu kayayyaki haraji ne da misalin karfe 11:45 na safe a yau, bayan da ya dawo ziyarar wani aiki a Hukumance daga Abuja. Da wannan sanya hannu, yanzu kudurin ya zama doka”, ya tabbatar.
Cikakken bayani na nan tafe.
Comments 1