Jami’an kwastam sun harbe wani mutum mai shekaru 35, Auwal Sani a kauyen Fadi Gurje, karamar hukumar Mani ta jihar Katsina ranar Juma’a.
Mazauna yankin sun shaidawa jaridar The Nation cewa, wasu jami’an kwastam sun afkawa ƙauyen a cikin motar sintiri, sannan suka fara harbi sama ba tare da wani dalili ba.
Rahotanni sun ce, wani mutum suna Sani ya samu rauni ne a kafarsa sanadiyar harin
Kazalika wasu Rahotanni sun ce, jami’an sun tsere a cikin hayaniyar da ta biyo bayan lamarin, kuma har yanzu ba a gano su ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masu Amfani da MTN na Fuskantar Matsalar Network
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, yayin tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa, ta ce, sun shiga tsakani tare da dawo da zaman lafiya a yankin.
Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ya kuma sanar da cewa, an kai mutumin da ya jikkata asibiti domin yi masa magani.
Comments 1